Attajirai za su ƙara yawa a Afirka cikin shekaru goma masu zuwa – Rahoto

Afirka Ta Kudu ce ke da kashi 34 cikin 100 na attajiran Afirka yayin da yawan attajiran Nijeriya ya ragu sosai, in ji Rahoton Arziƙin Afirka.

Newstimehub

Newstimehub

27 Aug, 2025

3c9d8cc5e74b48000381fd2cb0fae27e253d84d4c7b344c7e3cef671fb57cde4

Adadin yawan ‘yan Afirka masu miliyoyin daloli zai ƙaru da kashi 65 cikin 100 cikin shekaru goma masu zuwa, in ji Rahoton Arziƙi a Afirka na shekarar 2025.

A halin yanzu nahiyar na da attajirai na biloniyoyin daloli har mutum 25 da kuma mutum 348 masu aƙalla dala miliyan 100 da kuma mutum 122,500 masu aƙalla dala miliyan ɗaya, in ji rahoton shekara-shekara da kamfanin Henley & Partners mai sa ido a kan arziƙi ya wallafa.

An yi ƙiyasin cewa tattalin arziƙin Afirka ta Kudu da Hamadar Sahara zai ƙaru da kimanin kashi 3.7 cikin 100 a shekarar 2025 — inda za ta zarce Turai (mai kashi 0.7 cikin 100) da Amurka (mai cikin 1.4 cikin 100) — inda ake hasashen cewa girman tattalin arziƙi zai kai kashi 4.1 cikin 100 a shekarar 2026.

A halin yanzu Afirka ta Kudu ce ke da kashi 34 cikin 100 na masu dala miliyan ɗaya a Afirka — kusan daidai yawan attajiran ƙasashe biyar da ke biye da ita da yawan masu arziƙi a nahiyar — da masu aƙalla dala miliyan 41,100.