Uwargidan Shugaban Ƙasar Turkiyya Emine Erdogan ta bayyana a dandalin NSosyal ko NEXT Sosyal, sabon dandalin sada zumunta na ƙasar Turkiyya da aka kaddamar, tare da mika sakon jin daɗi da godiya.
“Barkanmu da war haka daga NSosyal. Na yi farin cikin kasancewa cikin wannan dandali namu na gida, na ƙasarmu, da masu zaman kansu, kuma ina mika godiyata ga duk wanda ya kawo wannan alfahari ga al’ummarmu,” ta faɗa a saƙonta na farko da ta wallafa a raar Talata.
A cikin wannan amintacciyar duniyar dijital tamu, za mu yi tunani da samarwa tare, da kuma tsara makomar gaba tare da dabi’unmu. Muna shirye don sabuwar tafiya tare da NSosyal.”
Hawanta dandalin na zuwa ne kwana guda bayan da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya bude nasa shafin a dandalin NSosyal.