Ana gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu jihohin Nijeriya

Manyan ‘yan siyasa irin su gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf da takwaransa na Kaduna Uba Sani da babban abokin hamayyarsa kuma tsohon gwamnan Jihar ta Kaduna Nasir El-Rufai duka sun yi yaƙin neman zaɓe ga ‘yan takarar jam’iyyunsu.

Newstimehub

Newstimehub

16 Aug, 2025

6b3a6ca53e7c6dcd014baef5e69d23dbf9315cbf5944983d8c38230d2a0318e4

A ranar Asabar ɗin nan ne ake gudanar da zaɓukan cike gurbi a wasu mazaɓu da ke sassa daban-daban a faɗin Nijeriya, waɗanda ake gani za su ƙara fito da ƙarfi ko akasin haka na Jam’iyyar APC mai mulki da kuma Jam’iyyun adawa na ƙasar.

Ana gudanar da zaɓukan ne a mazaɓu goma sha shida a jihohi 13 – Adamawa, Anambra, Edo, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Kogi, Neja, Ogun, Oyo,Taraba da Zamfara.

Zaɓukan da za a cike gurbinsu sun haɗa da na ‘yan majalisar dattawa da majalisar wakilai da majalisun dokoki na jihohi.