Ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 a Jamruriyar Nijar

A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliyar ruwa ta rusa gidaje 361.

Newstimehub

Newstimehub

15 Aug, 2025

f5b2297c0b58617d785b423991279fca1218793ad6f4d5d9eb846ae9e09b2ed8

Rahotanni daga Jamhuriyar Nijar na cewa ambaliyar ruwa ta kashe mutum 23 tare da jikkata 21 yayin da ta raba mutum 42,000 da gidajensu.

Kamfanin dillancin labaran ƙasar ya ruwaito cewa hukumar kwana-kwana ta ƙasar (GNSP) ce ta bayyana hakan a wani taron maneman labarai da ta gabatar ranar Alhamis.

A sanarwar da ta fitar a taron, GNSP ta ce ambaliya ta rusa gidaje 361. Sai dai ba ta faɗi lokacin da lamarin ya faru ba.

Kazalika GNSP ta tuna wa mutane shawarwarin da ta bayar a baya game da matakan da ya kamata a ɗauka wajen kauce wa hatsarin ambaliyar musamman ƙaurace wa tsallake gadajojin da ruwa ya rufe da kuma barin wuraren ambaliya da kuma rashin zama a gidaje masu rauni.