Isra’ila tana tattaunawa da ƙasashe hudu da yankin Somaliland wanda ya ɓalle daga Somaliya, domin bincika yiwuwar tilasta kwashe Falasɗinawa daga Gaza, kamar yadda kafafen yada labarai na Isra’ila suka bayyana a ranar Alhamis. Wannan mataki ya fuskanci suka sosai a matsayin take hakkin dokokin ƙasa da ƙasa.
Tashar Channel 12 ta Isra’ila ta ruwaito cewa an samu “ci gaba” a tattaunawa da Indonesia da Somaliland, wanda ya ɓalle daga Somaliya sannan ya ayyana ‘yancin kai a shekarar 1991 amma ba a amince da shi ba a hukumance.
Kafar ta bayyana sunayen Indonesia, Libya, Uganda, Sudan ta Kudu, da Somaliland a matsayin bangarorin da ke cikin tattaunawar.
Ta ambaci wata majiyar Isra’ila da ba a bayyana sunanta ba, wadda ta ce wasu ƙasashe sun nuna “alamun ƙofarsu a buɗe take” wajen karbar Falasdinawan da aka tilasta musu barin gidajensu saboda yakin Gaza, duk da cewa ba a cimma wata yarjejeniya ba tukuna.
A safiyar Alhamis, Sudan ta Kudu ce kadai ta mayar da martani a hukumance, inda ma’aikatar harkokin wajen ƙasar ta fitar da wata sanarwa a ranar Laraba tana ƙaryata rahotannin da ke cewa tana tattaunawa da Isra’ila, tana mai kiran su “marasa tushe” kuma ba su dace da manufofin ƙasar ba.