Babu ja da baya a dukkan matakan tabbatar da Turkiyya marar ta’adanci: Erdogan

Da zarar an cim ma manufar tabbatar da kasa da yanki marasa ta’addanci, za a bude sabon shafi ga kasar, in ji Shugaban Ƙasar Turkiyya.

Newstimehub

Newstimehub

7 Aug, 2025

0b8b97d56d31657578e6cc1127e0a682a05198b5fff33f1c99b74f419b549ab3

Babu kofar bayar da kai bori ya hau, ja da baya, sulhu ko wani yunkuri na sirri a matakin samar da Turkiyya marar ta’addanci, in Shugaban Kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a wata wasika da ya aike ga iyalan shahidai da ‘yan mazan jiya.

Erdogan ya jaddada cewa, duk wani taku na kasar nan cike yake da jinin shahidai da kuma ‘yan mazan jiya, yana mai cewa zaman lafiya, tsaro, da alfahari da Turkiyya ke samu a yau, sun samu ne saboda sadaukarwar da suka yi, kuma kare abin da suka bari shi ne babban aikin gwamnati.

“Ina roko da kuma kira gare ku da ku tabbata cewa babu wata kofa ta ja da baya ko bayar da kao bori ya hauc, tattaunawa, sasantawa da wani sirri a kowane lokaci a cikin wannan tsari, kuma ba za a samu damar yin hakan nan gaba ba.”

Ya kara da cewa “Babu wani mataki da aka dauka, kuma ba za a dauka ba, wanda zai azabtar da rayukan shahidanmu masu daraja ko cutar da iyalan shahidanmu da kuma tsaffin sojojinmu.”

Da zarar an cimma manufofin kasa da ba ta da ta’addanci, za a bude wani sabon babi ga kasar, in ji Erdogan, yana mai karawa da cewa: “’Yan uwantakarmu da ta shafe shekaru dubu za ta kai wani sabon mataki, kuma za a tumbuke tsagwaron sabani da aka shuka a tsakaninmu, kuma za a watsar da shi har abada.”

Erdogan ya kuma aike da wasika ga dukkan ‘yan kasar kan manufar tabbatar da kasar Turkiyya da ba ta da ta’addanci.

Ya ce, suna ci gaba da yin aiki tukuru don samar da wata kasa mai karfi da girma ta Turkiyya, tare da sanin cewa suna daukar nauyin kowane dan kasa a wuyayensu.

‘Daukar aniyar kawo karshen zubar da jini’