Ambaliya ta kashe wasu mutane a arewa maso gabashin Nijeriya

Ambaliyar da ta faru ta baya-bayan nan ta lalata wasu unguwanni a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Newstimehub

Newstimehub

28 Jul, 2025

1753682326889 51n1pe 73031591efc1775e558174b2ad248a539b9c558f30cfc5140b8ee8c94cbfd4e5

Wata mummunar ambaliyar da faru a arewa maso gabashin Nijeriya a ranar Lahadi ta kashe wasu mutane yayin da ta yi sanadin ɓacewar wasu gomman mutane.

Ambaliyar ta yi ɓarna a unguwannin Shagari da Yolde Pate da kuma Sabon Pegi a birnin Yola na Jihar Adamawa, inda ta kashe aƙalla mutum takwas, kamar yadda mazauna birnin suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.

Ambaliyar ta faru ne sakamako ruwan sama kaman da bakin ƙwarya na sa’o’i biyu da aka yi cikin dare, lamarin da ya sa bangwaye da gine-gine suka rushe kuma ruwa ya kwarara cikin gidaje.

Unguwannin da lamarin ya shafa suna fama matsalolin da ke biyo bayan ambaliya inda mazauna wurin da dama suka tsere daga gidajensu.

‘Waɗanda lamarin ya rutsa da su sun maƙale a gidajensu’

An ga mutanen birnin suna ɗaukar kayayyakinsu da ‘ya’yansu zuwa kan tudddai domin tsira.

“Ruwan saman ya lalata gidaje da yawa. Mun gano gawawwaki takwas, amma har yanzu ba mu san inda da yawa suke ba. Mutanen da suka mutu sun maƙale a cikin gidajensu yayin da suke jiran ruwa ya yi kasa,” kamar yadda wani mazaunin garin Banyawa Andrew ya shaida wa Anadolu.

Baya ga rayukan mutane, an rasa dabbobi ma.

Mai magana da yawun hukumar ba da agaji ta gaggawa ta ƙasa a Nijeriya (NEMA), Ibrahim Husseini, ya shaida wa Anadolu cewa hukumar tana yin “duk abin da za ta iya yi domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su tare da ba su agajin da ya kamata.”

Sai dai kuma bai ba da bayani ba game da yawan waɗanda ambaliyar ta kashe ko kuma waɗanda suka ɓace sakamakon ambaliyar ba. Gwamnatin jihar ba ta fitar da wata sanarwa ba game da ambaliyar da mace-mace da waɗanda suka ɓace da kuma ta’adin da ambaliyar ta yi a wurare cikin jihar Adamawa.

Daga farko dai NEMA ta yi gargaɗin cewa jihar Adamawa, tare da wasu jihohi za su fuskanci ambaliya a shekarar 2025. Bayan haka ne dai hukumar ta gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a watan Mayu domin ƙarin haske game da haɗɗuran ambaliya da kuma matakan da ya kamata a ɗauka domin tunkaran matsalolin sauyin yanayi.