Türkiye ta sake tabbatar da dangantakarta mai ƙarfi da Ƙungiyar Tarayyar Afirka a ranar bikin Ranar Afirka, inda ta ƙara jaddada shekaru ashirin na dangantaka.
“A wannan shekarar, muna murnar cika shekaru 20 da matsayin da Turkiyya ta samu na mai sa ido a Ƙungiyar Tarayyar Afirka,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a shafinta na X a ranar Lahadi.
Ma’aikatar ta kuma jaddada cewa Turkiyya tana daga cikin abokan haɗin gwiwa na musamman na Ƙungiyar Tarayyar Afirka.
“Muna shirin gudanar da Taron Ƙoli na huɗu na Haɗin Gwiwar Turkiyya da Afirka wanda za a yi a shekarar 2026,” in ji ta.
Ma’aikatar ta kuma taya murnar Ranar Afirka tare da cewa: “Barka da #RanarAfirka!”
A ranar Lahadi, ma’aikatar ta fitar da wata sanarwa daban a shafinta na yanar intanet don taya ƙasashen Afirka murnar Ranar Afirka.
“Ranar Afirka tana wakiltar burin al’ummomin Afirka na samun haɗin kai a cikin zaman lafiya, kwanciyar hankali da wadata, da kuma ƙudurin su na samun matsayi na adalci a tsarin duniya,” in ji sanarwar.
“Turkiyya za ta ci gaba da kasancewa amintacciyar abokiyar hulɗar ƙasashen Afirka a ƙoƙarinsu na cim ma waɗannan manufofin,” in ji ta.
Sanarwar ta bayyana aniyar Turkiyya ta ci gaba da ƙara yauƙaƙa dangantaka da ƙasashen Afirka, bisa tsarin “daidaito a ɓangaren ƙawance, amincewar juna da kuma cikakkiyar hadin gwiwa,” da kuma ci gaba da tuntuɓar ƙasashen Afirka.
“Türkiye da Afirka za su ci gaba da aiki tare don samun makoma ta bai ɗaya inda wadata, zaman lafiya da kwanciyar hankali za su tabbata,” in ji ma’aikatar.
Ranar Afirka tana wakiltar cika shekaru 62 da kafuwar Ƙungiyar Tarayyar Afirka.