Rundunar Sojin Nijeriya a ranar Lahadi ta ce ta rufe haramtattun matatun mai 19 a yankin Neja Delta a yunƙurinta na daƙile satar ɗanyen man fetur.
Laftanal Kanal Danjuma Jonah Danjuma, wanda shi ne mataimakin darakta na sashen hulɗa da jama’a na runduna ta shida ta sojin Nijeriya ne ya bayyana haka a wata sanarwa.
Ya bayyana cewa dakarunsu sun kai samame kan masu fasa-kwaurin man fetur ɗin daga 19 zuwa 25 ga watan Mayu, inda lamarin ya kai ga ƙwace kimanin lita 589,000 ta tataccen man fetur.
Haka kuma ya bayyana cewa dakarun nasu sun kama mutum 20 waɗanda ake zargi da hannu a wannan lamari.
Satar man fetur da kuma kai hare-hare kan bututan mai sun ja Nijeriya ta yi asarar fiye da dala biliyan uku a shekarar 2023 kaɗai, kamar yadda Sanata mai wakiltar Delta ta Arewa Sanata Ned Nwoko ya bayyana.
Sakamakon yadda Nijeriya ke da ɗanyen mai narke a cikin ƙasa wanda ya kai ganga biliyan 37, Nijeriya ce ta takwas a duniya ta ɓangaren ƙasashen da suka fi arziƙin man fetur sannan ita ce ta shida wadda ta fi fitar da mai.
Duk da haka, yankin na Neja Delta na yawan fama da rikice-rikice musamman na ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane da kuma fasa bututan mai.
Hakan ba shi rasa nasaba da kiraye-kirayen rashin adalcin da al’ummomin yankunan ke yi inda suke cewa ba su amfana da arziƙin da Allah Ya yi musu sannan kuma muhallinsu ya gurɓace.









