Erdogan ya karbi bakunci Firaministan Pakistan a Istanbul, ya yi alkawarin habaka alaka tsakanin su

Erdogan da Sharif sun tattauna a Istanbul don ƙara ƙarfafa alaƙar cinikayya da tsaro da haɗin kan yanki a tsakanin Turkiya da Pakistan.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2025

grzwvgaweaai74i

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan, ya karɓi Firaministan Pakistan, Shehbaz Sharif, a Fadar Shugaban Ƙasa ta Dolmabahce da ke Istanbul, yayin da shugabannin biyu suka sake jaddada aniyarsu na ƙarfafa haɗin kai a fannoni daban-daban.

Taron da aka gudanar ranar Lahadi ya mayar da hankali kan inganta dangantakar ƙasashen biyu da kuma tattauna manyan batutuwan yankin da na duniya, a cewar Sashin Sadarwa na Turkiyya.

Shugaba Erdogan ya jaddada muhimmancin aiki don cim ma burin ƙasashen biyu na faɗaɗa yawan cinikayya zuwa dala biliyan 5.

“Za mu ci gaba da ɗaukar matakai don cim ma burin cinikayya da kuma ƙarfafa haɗin kai a fannonin makamashi da sufuri da tsaro,” a kalaman Erdogan ga Sharif yayin tattaunawar, kamar yadda sashin ya bayyana.

Haɗin kaina kusa kan yaƙi da ta’addanci da haɗin kai

Shugaban Turkiyya ya jaddada muhimmancin ƙara haɗin kai a fannin yaƙi da ta’addanci, ciki har da musayar bayanan sirri da horo da tallafin fasaha. Ya bayyana cewa irin wannan haɗin kai yana da amfani ga dukkan ƙasashen biyu.

Yayin da yake bayani kan haɗa yankin, Erdogan ya nuna muhimmancin inganta da kuma tabbatar da aikin hanyar jirgin ƙasa na Istanbul–Tehran–Islamabad, yana mai cewa hakan zai iya ƙara haɓaka cinikayya da haɗin kai a yankin.

A fannin ilimi, shugaban Turkiyya ya yi kira da a ɗauki matakai na zahiri da za su ƙara ƙarfafa dangantakar kasashen biyu da kuma inganta musayar al’umma a dogon lokaci.

Matsayi ɗaya kan Falasɗinu da zaman lafiya na yankin

Shugaba Erdogan ya kuma nuna godiya ga matsayar Pakistan ta gaskiya kan batun Falasɗinu.

Ya yi wa Firaminista Sharif bayani kan ƙoƙarin da Turkiyya ke yi na tabbatar da cewa taimakon jin ƙai na gaggawa ya isa Gaza, a yayin da rikici ke ci gaba a yankin.

Taron shugabannin ya samu halartar manyan jami’an Turkiyya, ciki har da Ministan Harkokin Waje Hakan Fidan, da Ministan Tsaro Yasar Guler, da Daraktan Hukumar Leƙen Asiri ta Ƙasa (MİT) Ibrahim Kalin, da Shugaban Sashin Sadarwa Fahrettin Altun, da Babban Mai Ba da Shawara kan Harkokin Waje da Tsaro Akif Cagatay Kilic, da Kwamandan Rundunar Sojojin Ƙasa na Turkiyya Selcuk Bayraktaroğlu.

Ziyarar ta zama wani sabon babi a dangantakar ‘yan’uwantaka mai tsawo tsakanin Turkiyya da Pakistan, wadda aka gina bisa amincewa juna, da kusanci na al’adu, da haɗin kai mai ma’ana.