Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi watsi da rahotannin da ke cewa ta ƙi amincewa da gayyatar da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Nijeriya (INEC) ta yi mata domin sanya ido kan zaɓen ƙasar na shekarar 2027.
Jakadan Tarayyar Turai kuma shugaban Ofishin Wakilcin EU a Nijeriya da Ƙungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Gautier Mignot, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin ya bayyana cewa EU za ta tura tawaga mai ƙunshe da ƙwararru masu zaman kansu tsakanin biyu zuwa huɗu, domin girmama gayyatar da INEC ta aika mata a watan Afrilu.
Tun da farko, wasu rahotannin kafafen yaɗa labarai sun yi iƙirarin cewa EU ta yanke shawarar janyewa daga aikin sa ido kan zaɓen Nijeriya na 2027, lamarin da zai kawo ƙarshen kusan shekaru 20 da ta yi tana sa ido kan zaɓukan ƙasar.
Rahotannin sun danganta matakin da taɓarɓarewar tsaro da kuma zargin cewa an yi wa masu sa ido da jami’an EU wulaƙanci da nuna musu ƙiyayya lokacin da ƙungiyar ta sa ido kan zaɓen shekarar 2023.
Sai dai Mignot ya bayyana waɗannan rahotanni a matsayin “marasa inganci kuma na hasashe kawai.”
Ya ce shawarar EU kan girma da kuma tsarin tawagar da za ta tura domin sa ido kan zaɓe za ta dogara ne da yanayin da ake ciki a kowace ƙasa da kuma albarkatun da take da su.
“Tarayyar Turai tana yanke shawara kowace shekara kan tawagogin zaɓe da za a tura zuwa ƙasashen abokan hulɗa, bisa la’akari da gayyatar da ake yi wa EU, kuma idan shawarar ta kasance mai kyau, sai a tantance irin tawagar da za a tura zuwa kowace ƙasa, gwargwadon yanayin ƙasar da albarkatun da ake da su,” in ji Mignot.
EU ta musanta dalilan da aka danganta da rage yawan tawagar
Jakadan ya kuma yi watsi da dalilan da aka ruwaito cewa su ne suka sa aka yanke shawarar tura ƙaramar tawaga.
“Ofishin Wakilcin EU na ƙara jaddada cewa dalilai biyu da aka ambata a rahotannin kafafen yaɗa labarai ba su cikin wasiƙar. Waɗannan hasashe ne kawai.”
A baya, EU ta tura babbar Tawagar Masu Sa ido kan Zaɓe zuwa Nijeriya domin zaɓen gama-gari na shekarar 2023, inda ta fitar da shawarwari kan yadda za a inganta tsarin zaɓe a ƙasar.
Sai dai a zaɓen shekarar 2027, ƙungiyar za ta tura Tawagar Ƙwararrun Masu Sa ido kan Zaɓe, wadda za ta ƙunshi ƙwararru masu zaman kansu tsakanin biyu zuwa huɗu.
EU ta ce wannan matakin ba zai shafi ci gaba da goyon bayan da take bai wa tsarin dimokuraɗiyya da zaɓe a Nijeriya ba.















