Aƙalla mutum 570 sun rasa matsugunansu a birnin Kadugli da ke Kudancin Kordofan, a cikin kwana uku sakamakon tabarɓarewar yaƙi, a cewar wata saanrwa da Hukumar Kula da Masu Ƙaura ta Duniya (IOM) ta ranar Lahadi.
Sanarwar ta ce tawagoginta da ke bibiyar lamura a yankin sun shaida mata cewa mutum 570 sun tsere daga gidajensu a Kadugli daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Janairu, a yayin da hare-hare suka yi ƙamari a birnin.
Mutane sun nufi Jihar White Nile da ke Kudancin Sudan.
Halin da ake ciki a Kadugli yana cike da “rashin tabbas da hatsari,” a cewar OIM, inda ta ƙara da cewa tawagoginta suna ci gaba da sanya ido kan abubuwan d ke faruwa a yankin.
A makon jiya, IOM ta ce adadin mutanen da suka fice daga gidajensu a jihohi uku na Kordofan, Arewaci, Yammaci da Kudanci, ya ƙaru zuwa 64,890 daga ranar 25 zuwa 30 ga Oktoban 2025.













