Wasu abubuwa sun fashe a kusa da barikin soji a Abuja

Rundunar sojin ta sanar da hakan ne a shafinta na X a ranar Litinin, amma ba ta yi ƙarin bayani ba.

Newstimehub

Newstimehub

26 May, 2025

mogadishu

Rundunar sojin Nijeriya ta ce wasu abubuwa sun fashe a wata ƙaramar tashar bas da ke kusa da barikin sojoji a babban birnin tarayyar ƙasar a Abuja.

Rundunar sojin ta sanar da hakan ne a shafinta na X a ranar Litinin, amma ba ta yi ƙarin bayani ba.

Sai dai ta ce ana kan shawo kan lamarin, wanda ya faru a kusa d aBarikin Soji na Mogadishu.

Ita ma rundunar ‘yan sandan ƙasar ta sanar da cewa ta samu rahoton fashewar, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya sanar.