Wani abu ya fashe a Babban Asibiti a Jihar Kebbi ta Nijeriya

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi.

Newstimehub

Newstimehub

30 Dec, 2025

e9cefd860631d7d3d7ddd42a6ac84f66ece8868c5a6d9e4fcc848d19e5694cec main

Rundunar ‘yansandan Nijeriya reshen Jihar Kebbi ta tabbatar da fashewar wasu abubuwa a babban asibitin ƙaramar hukumar Bagudo da sanyin safiyar Talata.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kebbi, SP Bashir Usman Anisma, a wata sanarwa ya ce tawagar ƙwararru ta EOD-CBRN ta isa wajen don gudanar da cikakken bincike kan halin da ake ciki a asibitin.

Ya kuma tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata, amma wani gini a sashen gidajen ma’aikata na asibitin ya lalace, yayin da aka kwashe mutanen da ke cikinsa ba tare da matsala ba.

Kawo yanzu ba a san abin da ya yi sanadin fashewar ba, amma an soma gudanar da bincike, in ji shi.

Sai dai SP Usman ya ce Kwamishinan ‘yansandan Jihar ya tura ƙarin jami’an tsaro zuwa yankin dominn tabbatar da zaman lafiya.

‘Yansanda sun buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu su guji kusantar wajen don nuna goyon baya ga ayyukan tsaro da bincike da ake gudanarwa.