Gwamnatin Uganda ta yi watsi da zargin wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya da ke cewa sojojinta sun shiga hare-haren sama da suka jikkata fararen hula a Sudan ta Kudu. Rahoton kwamitin kare haƙƙin ɗan adam na MDD ya ce hare-haren hadin gwiwa tsakanin sojojin Sudan ta Kudu da na Uganda sun kai wuraren da galibin mazauna su daga kabilar Nuer ne.
Ma’aikatar tsaron Uganda ta musanta wannan zargi, tana cewa sojojinta ba su taɓa kai hari kan fararen hula ba a tarihin su. Ta jaddada cewa dakarun Uganda da ke Sudan ta Kudu suna taimakawa ne wajen hana tashin hankali da kuma kare rayukan jama’a.
Sojojin Uganda na cikin Sudan ta Kudu ne domin tallafawa gwamnatin Shugaba Salva Kiir a yaƙin da take yi da dakarun da ke goyon bayan jagoran ‘yan adawa Riek Machar. Machar dai an dakatar da shi daga mukamin mataimakin shugaban ƙasa a 2024 bayan fuskantar tuhume-tuhume na laifuka.
Sai dai rahoton MDD ya ce a wani hari da ya faru a Maris 2025 kusa da Juba, jiragen sama sun jefa wasu kwantena masu ɗauke da ruwa mai sa wuta wanda ya haddasa gobara tare da ƙone gidaje da jikkata fararen hula. Duk da haka, Uganda ta nace cewa dakarunta na aiki ne bisa yarjejeniyar tsaro da gwamnatin Sudan ta Kudu kuma ba su taɓa amfani da makaman sinadarai ko kai hari kan fararen hula ba.














