Rahotanni daga hukumar ƙwallo ta Turai, UEFA na cewa ta ci tarar ‘yan wasan Barcelona biyu, Lamine Yamal da Robert Lewandowski, tarar euro 5,000 kowannensu.
Wannan hukuncin na zuwa ne bisa laifin ‘yan wasan na rashin bin tsarin dokar hana shan ƙwayoyin ƙara kuzari a wasan da Barcelona ta buga na ƙarshe a gasar Zakarun Turai.
Laifukan sun auku ne a wasan Barcelona da Inter Milan a zagaye na biyu na wasan dab da na ƙarshe na gasar da aka buga a Italiya.
An tashi wasan ne da rashin nasara a ɓangaren Barca, inda ta sha kaye da ci 4-3 bayan ƙarin lokaci, wanda ya janyo aka fitar da su daga gasar da PSG ta ɗaga kofin a ƙarshe.