Turkiyya ta yi tur da harin da Isra’ila ta kai kan tawagar Hamas a Qatar

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta yi kakkausan gargaɗi da yin tur da “manufofin Isra’ila na faɗaɗa mamaya.”

Newstimehub

Newstimehub

10 Sep, 2025

2ce28764fac3fdad3211a2b9663585c6c475465ff4d2deade03d6cadd7328f00

Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar da wata sanarwa mai lamba: 183, a ranar 9 ga Satumban 2025, “Dangane da Harin Isra’ila kan Doha, Babban Birnin Qatar”.

“Muna Allah wadai da harin da Isra’ila ta kai kan tawagar tattaunawar Hamas a Doha, babban birnin Qatar,” sanarwar ta fara da cewa.

Ma’aikatar ta nuna cewa ayyukan Isra’ila suna da rikitarwa; a gefe guda tana nuna kamar tana son tattaunawa don kawo karshen yakin Gaza da dawo da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su, amma a gefe guda tana ƙara tayar da tarzoma har ma a wasu yankunan da ba na Falasdinu.

“Kai hari kan tawagar tattaunawar Hamas yayin da ake ci gaba da tattaunawar tsagaita wuta yana nuna cewa Isra’ila tana son ci gaba da yaƙi, ba zaman lafiya take nema ba.”