Jami’an tsaron Turkiyya sun kama mutane 30 ciki har da wani da ake zargin jagoran wata babbar ƙungiyar masu aikata laifuka ne, Alihan Kuris, yayin wani samame da aka kai kan ƙungiyar masu aikata laifuka mai suna “Alihan Kuris Criminal Organisation”, kamar yadda Ofishin Babban Mai Shigar da Ƙara na Ankara ya bayyana ranar Alhamis.
A cewar sanarwar ofishin mai shigar da ƙarar, Hukumar Binciken Laifukan Kuɗi ta Turkiyya (MASAK) ta shirya wani rahoto kan waɗanda ake zargin da kuma kamfanonin da ke da alaƙa da ƙungiyar, a wani bincike da ya shafi zarge-zargen da suka haɗa da kafa da jagorantar ƙungiyar masu aikata laifuka, kasancewa mamba a ƙungiyar masu aikata laifuka, halatta kuɗaɗen haram, damfarar cibiyoyin gwamnati da kuma karya dokar haraji.
A cewar rahoton MASAK, yawan hada-hadar kuɗaɗen kamfanoni da dama da ke da alaƙa da ƙungiyar ya ƙaru sosai bayan shekarar 2020, yayin da aka rarraba wasu kamfanonin tare da mayar da ikon mallakarsu.
Rahoton ya gano cewa an kafa wasu sabbin kamfanoni da jari mai kauri ta hanyar rarraba tsoffin kamfanoni, sannan aka kafa waɗannan sabbin kamfanoni a wasu larduna daban-daban tare da gudanar da harkokin da suka bambanta da na kamfanonin da aka samar da su daga gare su.
A cewar rahoton, wasu daga cikin kamfanonin ba su da wasu kadarori ko albarkatu face jarinsu, kuma ba sa gudanar da harkokin kasuwanci kai tsaye, sai dai suna amfani da jarin wajen tallafa wa wasu kamfanonin da ke ƙarƙashinsu.
Rahoton ya ce ana zargin ƙungiyar da amfani da wannan tsari ne domin hana samun damar duba bayanan kamfanonin da kuma ƙara wahalar bin diddigin hada-hadar kuɗaɗensu.
Rahoton ya kuma gano cewa yawancin kamfanonin sun karɓi kuɗaɗe ta wasu cibiyoyin biyan kuɗi daban-daban, sannan suna yawan yawo da tsabar kuɗi. Masu hannun jarin kamfanonin kuma sun yi zuba jari mai kauri na tsabar kuɗi waɗanda ake buƙatar bayyana tushensu.
Daga baya, an yi amfani da waɗannan kuɗaɗen da masu hannun jarin suka zuba wajen ƙara jarin kamfanonin.
Rahoton ya ƙara da cewa an riƙa tura manyan kuɗaɗe da aka saka cikin asusun kamfanonin zuwa wasu kamfanonin da ake bincike, yayin da aka kuma tura manyan kuɗaɗen da aka samu ta cibiyoyin biyan kuɗi da kuma ajiyar tsabar kuɗi zuwa wasu kamfanoni daban-daban.
Rahoton ya bayyana cewa bayanan saye da sayarwar kamfanonin sun nuna yadda aka rinƙa hada-hadar kuɗi sosai da wasu kamfanoni masu rijista, yana mai cewa irin waɗannan hada-hadar na iya kasancewa da alaƙa da fitar da takardun biyan kuɗi na bogi.
Haka kuma, an gano yadda aka rinƙa tura wasu kuɗaɗen kasashen waje daga kamfanoni daban-daban da ke ƙetare waɗanda ba su dace da bayanan kamfanonin ba. Wasu kamfanonin kuma sun karɓi manyan kuɗaɗen mayar da haraji.
Rahoton ya tantance cewa wataƙila an gudanar da waɗannan hada-hadar kuɗi ne cikin tsari mai kyau da haɗin gwiwa.
A wani ɓangare na binciken, an gudanar da samame lokaci guda kan ƙungiyar Alihan Kuris a larduna 17, musamman a Istanbul, Ankara da Antalya.
Hukumomi sun bayar da umarnin kama mutane 49, waɗanda ake zargi da hannu a ƙungiyar. An gano cewa wasu daga cikinsu suna ƙasashen waje. Haka kuma, an bayar da sammacin bincike da kwace wasu kadarori a adireshi 43 da ke da alaƙa da waɗanda ake zargin, da kuma adireshi 80 na kamfanoni 33.
Daga cikin mutane 49 da aka bayar da umarnin kama su, an kama 30, ciki har da Alihan Kuris, yayin samamen.
An gano cewa mutane tara suna ƙasashen waje, yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da ƙoƙarin kama sauran mutane 10.














