Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Isra’ila na so ta faɗaɗa shirinta na kisan ƙare-dangi a Gaza amma mahukunta a Ankara za su ci gaba da yaƙi da wannan shiri tare da haɗin gwiwa da Pakistan.
A yayin da yake ganawa da Firaministan Pakistan Shahbaz Sharif ranar Lahadi a birnin Tianjin na ƙasar China, Erdogan ya ce matsayin Turkiyya irin na Pakistan ne na yaƙi da kisan ƙare-dangi da Isra’ila take yi, a cewar wata sanarwa da Sashen Watsa Labarai na Gwamnatin Turkiyya ya wallafa a shafin sada zumunta na NSosyal.









