Turkiyya ba za ta taɓa yin shiru game da zaluncin Netanyahu kan Falasɗinawa ba: Erdogan

“Duk da rashin adalci da zalunci da ake yi a yankinmu, ba za mu taɓa yanke ƙauna ba,” a cewar shugaban Turkiyya.

Newstimehub

Newstimehub

4 Sep, 2025

d80f1889879053952c2e1a5c643c751ad34311982eff4f9a711831c9f5464aeb

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada cewa ƙasarsa ba za ta taɓa zuba ido tana kallo ana cutar da Falasɗinawa da hare-haren Isra’ila ba, inda ya caccaki Firaminista Benjamin Netanyahu.

“Ba za mu ci gaba da yin shiru tare da zuba ido game da irin wahalhalun da Netanyahu ya yake jefa Falasɗiawa a ciki ba,” in ji Erdogan a ranar Laraba, yayin da yake jawabi a makon buɗe taron Maudili a Ankara.

Shugaban ya ƙara da cewa damuwar Turkiyya ta wuce iyakokinta, yana mai jaddada haɗin kai domin ceto ƙasashen Musulmai da ke fama da tashe-tashen hankula.

“Rabin zuciyarmu yana nan; sauran rabin kuma yana Gaza da Falasɗinu da Yemen da Sudan da kuma Afghanistan, inda al’ummar Musulmai suke jin raɗaɗin rauni da kuma jinin da ake zubarwa,’’ in ji shi shugaban.

Da yake jaddada muhimmacin haɗin kai, Erdogan ya bayyana cewa: “Muna ɗaukar dukkan Musulmai a matsayin tubalin gini iri ɗaya, wato sassan jiki ɗaya.”

Duk da tashe-tashen hankula a yankin, shugaban ya buƙaci jajircewa da kuma tsayin-daka kan gaskiya.