Wata kotu ta yanke wa Jean-Guy Mayolas, tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Jamhuriyar Congo, hukuncin daurin rai da rai bayan same shi da laifukan wanke kudade, kirkirar takardu na bogi da kuma karkatar da kudaden hukuma. An yanke hukuncin ne a bayan kotu bayan Mayolas bai bayyana a gaban kotu ba, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Masu gabatar da kara sun ce Mayolas ya karkatar da kusan dala miliyan 1.1 daga kudaden da FIFA ta bayar domin bunkasa kwallon kafa a kasar. Cikin kudaden har da tallafin dala 500,000 da aka ware domin inganta kwallon kafa ta mata bayan annobar COVID-19. Hukumomi sun ce an yi alkawarin shirya gasar mata da kuma inganta filayen wasanni, amma ba a aiwatar da wadannan ayyuka ba.
Wasu abokan aikinsa ma sun fuskanci hukunci a shari’ar. Ɗansa Lionel Mayolas shi ma an yanke masa hukuncin daurin rai da rai, yayin da wasu jami’an hukumar kwallon kafa Badji Mombo Wantete da Raoul Kanda aka yanke musu hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari saboda rawar da suka taka a lamarin.
Wannan badakalar ta biyo bayan rikici tsakanin gwamnatin Congo da hukumar kwallon kafa. A shekarar 2024 gwamnati ta cire Mayolas daga mukaminsa, lamarin da ya sa FIFA ta dakatar da hukumar kwallon kafar kasar saboda zargin tsoma bakin gwamnati. Dakatarwar ta sa tawagar kwallon kafar kasar ta rasa damar buga wasanni biyu na neman tikitin gasar cin kofin duniya ta 2026 kafin daga bisani a dage dakatarwar a watan Mayu.














