Tsohon firayim ministan Burundi, Alain-Guillaume Bunyoni, ya samu ‘yancin fita daga kurkuku na wucin gadi saboda matsanancin rashin lafiya da ake cewa ta tsananta a baya-bayan nan. Bunyoni yana zaman hukuncin ɗaurin rai da rai ne bayan an same shi da laifi a wani shari’a da ta shafi zargin yunkurin juyin mulki kan Shugaba Evariste Ndayishimiye.
A baya Bunyoni ya rike manyan mukamai a gwamnatin Burundi, ciki har da shugaban ‘yan sanda, ministan tsaron cikin gida da kuma firayim minista tsakanin 2020 zuwa 2022. Majiyoyin shari’a sun ce kotu ta amince da sakin nasa na wucin gadi saboda dalilan lafiya bayan an nuna damuwa kan tabarbarewar lafiyarsa.
Kungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam sun ce Bunyoni na fama da matsananciyar cutar sukari, kuma lafiyarsa ta kara tabarbarewa a lokacin da yake tsare saboda ƙarancin kulawar lafiya. Rahotanni sun kuma ambaci cewa ya fuskanci matsalolin motsi da kuma wahalar magana.
Tun watan Oktoba aka kwantar da shi a asibiti kafin daga bisani hukumomi su ba shi damar komawa gidansa da ke Bujumbura. Iyalansa sun ce har yanzu yanayin lafiyarsa na da matuƙar damuwa, yayin da ba a san tsawon lokacin da wannan sakin na wucin gadi zai ɗauka ba.














