Shugaba Bola Tinubu ya amince da a ƙara saka wasu asibitocin gwamnatin tarayya a tsarinsa na rage kuɗin wankin ƙoda daga ₦50,000 zuwa ₦12,000 wanda ya fara sanarwa a watan Maris ɗin wannan shekarar.
Mai bai wa Shugaban Ƙasar Shawara na Musamman kan Manufa da Watsa Labarai, Daniel Bwala ne ya bayyana hakan a shafinsa na X ranar Litinin.
Ya bayyana cewa “da wannan daukin, kuɗin kowane aiki na wankin ƙoda ya ragu daga N50,000 zuwa N12,000 kacal, lamarin da zai kawo sauƙi ga dubban ‘yan ƙasa da ke fama da cututtukan da suka shafi ƙoda.”
Bwala ya ce tuni an riga an fara aiwatar da tallafin a muhimman asibitocin gwamnatin tarayya 10 a shiyoyin ƙasar shida.
Asibitocin sun haɗa da Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Ebute-Metta, a Legas; da Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Jabi a Abuja; da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan; da kuma Cibiyar Lafiya ta Gwamnatin Tarayya da ke Owerri.