Shugaba Bola Tinubu a ranar Juma’a ya yi alkawarin hanzarta ƙera makamai da harsasai a cikin gida domin ƙarfafa tsarin tsaron Nijeriya.
Yayin da yake jawabi a Abuja a lokacin bikin kammala karatun Course 33 na Kwalejin Tsaro ta Nijeriya da ke Abuja, wanda mataimakinsa Kashim Shettima ya wakilta.
Ya bayyana cewa ƙara ƙarfin masana’antu na cikin gida zai rage dogaro da masu kaya na ƙasashen waje, sannan zai inganta yaki da rashin tsaro a ƙasa.
Daliban na Course 33 sun fito ne daga sojojin ƙasa da na ruwa da na sama na Nijeriya da sauran hukumomi daga ciki da wajen Nijeriya.
Shugaban ya nuna farin ciki da taken na Course 33 na kwalejin, “Karfafa Hukumomi Don Tsaro da Ci Gaban Nijeriya,” yana mai cewa tushe na kowace al’umma mai nasara shi ne hukumomi masu ƙarfi da juriya.