Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce amince ma’aikatar tsaron ƙasar ta sayi ƙarin jirage mara matuƙa domin yaƙi da ‘yan bindiga a Jihar Katsina da sauran sassan ƙasar.
Wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata da maraice ta ce shugaban na Nijeriya ya kuma bayyana cewa za a ƙara yawan dakaru a Jihar Katsina domin hana kai hare-hare kan ‘yan ƙasa da ba su ji ba ba su gani ba.
Shugaban ya bayyana wannan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar manyan ‘yan jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Dikko Umaru Radda.
Sanarwar ta ambato Shugaba Tinubu yana cewa: “Yau na ba da umarni ga dukkan jami’an tsaro su ƙarfafa [ayyukansu] su kuma sake nazari kan dabarun yaƙi. Mun amince a sayi ƙarin jirage mara matuƙa.”
“Ƙalubalen da muke fuskanta abubuwa ne da za mu iya cin galaba a kansu. Da gaske muna da iyakoki da babu tsaro. Mun gaji da wannan rauni, ya kamata a ce an magance wannan matsala kafin yanzu. Ƙalubale ne da ya zama dole mu magance shi, kuma muna tunkararsa,” in ji Tinubu.