Tarayyar Turai ta amince da wani sabon gyara a tsarin kwastam nata, wanda zai kawo sabbin kuɗaɗen sarrafawa kan ƙananan kayayyakin da ake shigowa da su daga waje. Manufar wannan mataki ita ce daidaita kasuwancin intanet da kuma ƙarfafa bincike kan yawan kayayyakin da ke shigowa Turai, musamman waɗanda darajarsu ba ta da yawa amma sun ƙaru sosai a cikin shekaru na baya-bayan nan.
Sabbin kuɗaɗen za su zo ne baya ga harajin euro 3 a kowane kunshi da aka riga aka tsara fara aiwatarwa daga watan Yulin 2026, tare da yiwuwar ƙarin kusan euro 2 a kan kowane kaya domin tallafa wa ayyukan kwastam. Wannan tsarin ya fi karkata ne kan manyan dandamalin kasuwanci kamar AliExpress, Temu da Shein, waɗanda ke aika ƙananan kaya masu araha kai tsaye zuwa ga masu saye a Turai.
Sabon tsarin ya kuma tanadi cewa waɗannan dandamali za su ɗauki alhakin kayayyakin da ake sayarwa a shafukansu, ta fuskar doka da ma laifi idan an ci gaba da karya ƙa’idojin Turai. Hukumomi na kuma tunanin kakaba tarar kuɗi ko ma dakatar da ayyukansu a cikin EU idan aka samu maimaita laifi. Baya ga haka, ana son a sauya yadda ake shigo da kaya ta hanyar ƙarfafa kamfanoni su rika kawo kayayyaki da yawa a lokaci guda, su biya haraji tun kafin rabawa, sannan su ajiye su a cikin Turai kafin su kai ga masu amfani.
Gyaran ya kuma haɗa da sabbin hanyoyi na zamani kamar kafa cibiyar bayanai guda ɗaya da za ta tattara dukkan bayanan zirga-zirgar kasuwanci, da kuma sabuwar hukuma mai suna EU Customs Authority da za ta kula da haɗa kai tsakanin ƙasashen mambobi wajen bincike da sarrafa haɗari. Tarayyar Turai ta ce wannan shi ne mafi girman sauyi a tsarin kwastam nata cikin fiye da shekaru 50, kuma za a fara aiwatar da shi a hankali daga 2026, tare da cikakken aiwatarwa nan da 2028.














