Sojojin Somaliya sun kashe wanda ya shirya yunƙurin kashe Shugaba Hassan Sheikh

Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Somaliya (NISA) ta sanar da cewa dakarunta sun kashe Mohamed Abdi Dhiblaawe Afrax, wani babban kwamandan ƙungiyar Al-Shabaab.

Newstimehub

Newstimehub

11 Sep, 2025

1753465147215 b4i97d 88383b83cd60de8985e21c571933d626a316d476cdbdda3191fba17e3c2134fc

Hukumar Leken Asiri da Tsaro ta Somaliya NISA ta sanar da cewa dakarunta sun kashe Mohamed Abdi Dhiblaawe Afrax, wani babban kwamandan ƙungiyar Al-Shabaab, a wani samame da suka shirya yi a Ugunji, da ke yankin Lower Shabelle.

Hukumar ta NISA ta tabbatar da cewa Afrax ne ya shirya yunkurin kisan gillar da bai yi nasara ba a kan ayarin motocin Shugaban Ƙasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud a ranar 18 ga Maris ɗin 2025.

Harin 18 ga Maris na 2025

Da misalin ƙarfe 10:32 na safiyar ranar ne aka kai wa ayarin motocin shugaban hari a kusa da mahadar El-gaabta da ke gundumar Xamar-Jajab, a lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama domin tafiya tare da dakarun sa-kai na Hirshabesha.

Daya baya ma’aikatar yada labaran ƙasar ta tabbatar da cewa an daƙile harin, kuma shugaban ya isa inda ya yi niyyar zuwa.