Rundunar sojin ruwan Nijeriya ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da ƙoƙarin tserewa zuwa Turai ta hanyar ɓoye a cikin jirgin ruwa a tashar jiragen ruwan Legas. An gano su ne a cikin wani ɓangare na jirgin MV Seaspan Lahore yayin binciken yau da kullum da jami’ai ke yi kafin tafiya.
An bayyana sunayensu da Abdullahi Yakubu mai shekara 36 da Omoniyi Afotona mai shekara 25. Daga baya an miƙa su ga jami’an hukumar shige da ficen Nijeriya da ke Apapa domin ci gaba da bincike da kuma yiwuwar gurfanar da su a gaban kotu.
Kwamandan rundunar NNS BEECROFT, Commodore A. Adams-Aliyu, ya ce an kama su ne da sanyin safiyar ranar 19 ga Maris 2026 yayin da jirgin ke shirin tashi. Ya bayyana cewa irin wannan hanya ta shiga jirgi a ɓoye ba bisa ƙa’ida ba tana da haɗari sosai kuma ta saba wa doka.
Ya kuma yi kira ga matasa su guji irin wannan tafiya mai hatsari, yana mai jan hankalin iyaye su wayar da kan ‘ya’yansu, tare da ƙarfafa masu neman zuwa ƙasashen waje su bi hanyoyin da suka dace.













