Sojojin Nijeriya Sun Daƙile Harin ISWAP a Yobe, Sun Kashe Fiye da 20

Sojojin Nijeriya sun dakile wani hari na ISWAP a Goniri, Jihar Yobe, inda suka kashe fiye da ’yanta’adda 20 tare da kwato makamai bayan artabu mai tsanani.

Newstimehub

Newstimehub

13 Mar, 2026

2026 02 03t182206z 1 lynxmpem12167 rtroptp 3 usa trump nigeria 1

Sojojin Rundunar Haɗin Gwiwa ta Nijeriya ƙarƙashin Operation HADIN KAI sun daƙile wani hari da ake zargin mayakan ISWAP ne suka kai kan sansanin sojoji a Goniri da ke Jihar Yobe. Harin ya faru ne daga daren Litinin zuwa wayewar garin Talata, inda maharan suka yi ƙoƙarin kewaye sansanin daga bangarori da dama.

Majiyoyin tsaro sun ce an gano motsin maharan tun da wuri ta hanyar na’urorin sa ido yayin da suke tahowa daga ƙauyen Goniri da kuma hanyar Ngamdu junction. Da zarar an gano su, sojojin suka mayar da martani tare da tura ƙarin dakarun taimako da kuma jiragen yaƙi domin kare sansanin.

Jiragen yaƙi na rundunar saman Nijeriya sun ba da tallafi daga sama, wanda ya tilasta wa ’yan ta’addan janyewa bayan sun yi asara mai yawa. Aƙalla ’yanta’adda sama da 20 aka kashe, ciki har da wani babban kwamandansu mai suna Abu Yusu, yayin da sojojin suka ƙwato makamai da bama-bamai da maharan suka bari.

Bayan artabun, sojoji sun ci gaba da sintiri a yankunan da ke kusa, musamman a Timbuktu Triangle da Gwaigomari, inda aka sake gano wasu gawarwakin ’yan ta’addan. An kuma tabbatar da cewa wasu daga cikin sojojin Nijeriya sun ji rauni, amma suna samun kulawar likitoci yayin da dakarun ke ci gaba da bincike domin kamo waɗanda suka tsere.

Majiyar Labari: NEWSTIMEHUB