Rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta na Birged ta 13, sun yi nasarar ceto mutum 18, ciki har da ƙananan yara biyu, bayan ‘yanbindiga sun yi garkuwa a kwalekwale yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Kamaru.
Wata sanarwa da mataimakin mai magana da yawun Birged ta 13 Manjo Yemi Sokoya ya fitar ranar Litinin ta ce lamarin ya faru ne ranar Lahadin da ta wuce.
Ya ƙara da cewa wasu da ake zargi ‘yanfashin teku ne a cikin kwalekwale guda biyu masu gudun tsiya da kwalekwale na katako sun yi garkuwa da wani kwalekwalen da ke ɗauke da fasinjoji da ya kama hanya daga Nijeriya zuwa Kamaru.
‘Yanfashin sun sace mutanen ne a gaɓar tekun da ake kamun kifi mai suna Kombo Fishing Port da ke ɓanagren Kamaru.
Manjo Sokoya ya ce nan-take dakarun Birged ta 13 da ke aiki a Ikang suka bi sawun ‘yanfashin tekun, inda suka yi ta musayar wuta lamarin da ya sa ɗaya daga cikin kwalekwalensu ya kife.
Daga nan ne ‘yanfashin tekun suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su inda suka tsere cikin wani daji da ke kusa, in ji sanarwar inda ta ƙara da cewa “an ceto dukkan fasinjojin ba tare da sun samu ko da ƙwarzane ba.”









