Shugaban Turkiyya Erdogan ya tafi Qatar don halartar taron Ƙasashen Larabawa da Musulmai

Qatar ce ta kira taron ƙolin a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai wa shugabannin Hamas a Doha a makon jiya, inda aka kashe mambobin ƙungiyar biyar da jami’in tsaron Qatar guda ɗaya.

Newstimehub

Newstimehub

15 Sep, 2025

acf6c5877e896e9d00ad664d0f3016b26372a3c38d1953cb7e953eae416df861

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya soma wata ziyara a Qatar a ranar Litinin, inda zai halarci taron gaggawa na Ƙasashen Larabawa da Musulmai da za a gudanar bayan harin da Isra’ila ta kai a Doha a makon jiya.

Shugaba Erdogan ya samu rakiyar matarsa Emine Erdogan, da shugaban hukumar leƙen asiri ta ƙasa (MIT) Ibrahim Kalin, da Akif Cagatay Kilic, da kuma babban mai bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Ƙasashen Waje da Tsaro, Daraktan Dadarwa Burhanettin Duran, da Mataimakin Shugaban Jam’iyyar Justice and Development (AK) Halit Yerebakan.

Taron Ƙasashen Larabawa da Musulmai a birnin Doha ya hada shugabannin ƙasashe da manyan jami’ai da dama daga sassan yankin.

Qatar ce ta kira taron a matsayin martani ga harin da Isra’ila ta kai kan shugabannin Hamas a Doha a makon jiya, inda aka kashe mambobin kungiyar biyar da jami’in tsaron Qatar guda ɗaya.