Shugaban ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a hedkwatar rundunar sojin da ke birnin Accra yayin taron 2025 West African Soldiers’ Social Activity (WASA).
Taron WASA ana shirya shi ne duk shekara a matsayin wani taron liyafa ga sojoji kasar don samu gana da juna da yaba wa juna.
Sojojin sun fashe da shewa da tafi jim kadan bayan da shugaban kasar ya sanar da su batun karin albashin yayin da yake jawabi a wajen taron.
“Ina take da wani abin farin ciki kuma ina farin cikin sanar da ku cewa sabon tsarin albashi zai fara aiki a watan Maris. Na ce abin farin ciki. Yanzu na san kun fahimci abin da nake nufi. Sabon tsarin zai fara aiki a watan Maris, kuma za biya ku karin watan Janairu da na Fabrairu,” in ji Shugaba Mahama.
Shugaban ya ce shekaru hudu bayan shekarar 2020, gwamnatin da ta gabata ba ta yi wani tanadi ba ta fuskar kudi da dangane da sabon tsarin kudin gratuti.
Ya ce sakamakon haka an samu tarin ma’aikata da suke bin bashi wanda ya wuce cedi biliyan daya, inda jimillar ma’aikata kimanin 3,000 suke bin bashi masu mukamai daban-daban.
Shugaban kasar ya ce yanzu ya umarci Ma’aikatar Kudi ta biya sojojin da suka yi ritaya sabon tsarin gratuti da suke bi bashi, wadanda suke shekara 95 zuwa 96 a duniya. Sannan ya ce a daya bangaren kuma an fara shirye-shiryen biyan saura.









