Shugaban kasar Congo-Brazzaville, Denis Sassou Nguesso, ya sake lashe zaben shugaban kasa da kusan kashi 95% na kuri’un da aka kada, kamar yadda sakamakon wucin gadi ya nuna. Wannan nasara ta kara masa wa’adi na shekaru biyar, tare da tsawaita mulkinsa wanda ya shafe kusan shekaru arba’in yana rike da iko a kasar mai arzikin mai.
Ministan harkokin cikin gida, Raymond Zephyrin Mboulou, ya bayyana cewa Sassou Nguesso ya samu kashi 94.8% na kuri’u, yayin da yawan masu kada kuri’a ya kai kashi 84.65%, duk da hasashen da aka yi na raguwar masu fitowa zabe. Sai dai ana jiran kotun kundin tsarin mulki ta tabbatar da wannan sakamako kafin a kammala shi.
Duk da cewa ‘yan takara shida sun fafata da shi, babbar adawa ta kasance rarrabuwa kuma ba ta fito da karfi ba. A yayin yakin neman zabensa, shugaban mai shekaru 82 ya jaddada nasarorin tattalin arziki, musamman a bangaren gyaran ababen more rayuwa da bunkasa gas da noma domin cimma dogaro da kai.
Sassou Nguesso ya kuma ce ba zai ci gaba da mulki har abada ba, yana mai nuni da cewa tsarin mulki ya hana shi sake tsayawa takara a 2031. Duk da haka, bai bayyana wanda zai gaje shi ba. Shugaban ya taba mulkar kasar tun 1979, sannan ya dawo kan karagar mulki bayan yakin basasa a 1997, kuma tun daga nan yake ci gaba da lashe zabuka daban-daban.














