Saif al-Islam Gaddafi: An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi

An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi a birnin Zintan da ke yammacin Libya, kamar yadda lauyansa Khaled al-Zaidi da mai ba shi shawarwari Abdullah Osman suka bayyana.

Newstimehub

Newstimehub

4 Feb, 2026

2026 02 03t194010z 1 lynxmpem1218k rtroptp 3 libya security gaddafi

An kashe ɗan marigayi shugaban Libya Muammar Gaddafi, Saif al-Islam Gaddafi, mai shekara 53, kamar yadda majiyoyin da ke kusa da iyalinsa suka bayyana, in ji lauyansa Khaled el-Zaydi da kuma kafofin watsa labaran Libya.

Mai ba shi shawarwari Abdullah Osman ya tabbatar da mutuwarsa ranar Talata.

Kafafan watsa labaran Libya sun ba ta rahoton cewa kisan ya faru ne a gidansa kuma mutum huɗu ba a san ko wanene su ba, suna masu ƙrawa da cewa, an kashe kamarorin sa ido a wurin kafin a kai harin.

Ofishin babban lauyan Libya ya fara bincike game da kisan, in ji kafafen watsa labaran ƙasar.

Kawo yanzu dai bayanai game da kisan Saif al-Islamna da sarƙaƙiya kuma hukumomin Libya ba su fitar da bayani a hukumance da zai tabbatar da lamarin ba.

Ta shafinsa na Facebook, Moussa Ibrahim, wani stohon mai magana da yawun Gaddafi, ya rubuta cewa: “Sun kashe shi cikin hai’inci yayin da yake son samar da haɗaɗɗiyar Libya mai ‘yancin kai da zai tsare dukkan mutanenta … Sun kashe fata da kuma wata makoma kuma sun shuka ƙiyayya da gaba.”

Game da kisan gillan da aka masa, Ibrahim ya ce: “Manufar ita ce ƙarin zubar da jini da raba Libya da kuma lalata dukkan shirin haɗin kan ƙasa, inda yake kare muradun baƙi a ƙasar.”

Kamfanin dillancin labaran Libya ya ambato “birged na 444” da ke da alaƙa da ma’aikatar tsaron gwamnatin haɗin kan ƙasa inda ya musanta “kai-tsaye” abin da ake yayatawa a kafafen sada zumunta game da alaƙarta da da arangamar da suka faru a birnin Zintan da kuma labarin da ya biyo shi game da kisan Saif al Islam.

Tun da aka kama shi tun byan an yi juyin-juya-hali na makamai da ya hamɓarar da gwamnatin mahaifinsa a shekarar 2011, Saif-al-Islam ya kasance yana zaune a birnin Zintan, da ke da nisan kilomita 136 ( mil 85 ) kudu maso yammacin babban birnin ƙasar Tripoli, amma babu wanda ya san inda yake bayan an sake shi a shekarar 2017.