Shugaba John Mahama ya tattabar wa mutanen ƙasarsa cewa rundunar sojin ƙasar za ta gudanar da cikakken bincike kan abin da ya janyo hatsarin helikwaftan da ya kashe ministoci biyu da wasu jami’a gwamnatin Ghana.
Da yake jawabinsa na farko tun bayan hatsarin a fadar gwamnatin ƙasar ranar Alhamis, Shugaba Mahama ya bayyana alhininsa tare da miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su
Ya ce duk da cewa al’umar ƙasar na son sanin abin da ya janyo hatsarin, ya kamata ‘yan ƙasar su haɗa kai a wannan lokacin makokin.
“Yayin da muke juyayi, dole mutane za su yi ta tambaya game da silar wannan bala’in kuma [tambayoyin] na da muhimmanci.,” in ji shi.
Shugaba Mahama ya jaddada jajircewar gwamnatin wajen gano gaskiyar abin da ya janyo hatsarin, yana mai tabbatar wa ‘yan ƙasar Ghana cewa babu wani bayanin da za a ɓoye musu.