Ofishin Babban Mai Bai wa Shugaban Nijeriya Shawara kan Tsaro Malam Nuhu Ribadu ya mayar wa tsohon Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai martani dangane da wata hira da El-Rufai ya yi da gidan talabijin na Channels TV ranar Lahadi.
Tsohon gwamnan, wanda ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC kuma ya koma hadakar ’yan adawa ta ADC, ya yi zargin cewa gwamnatin Jihar Kaduna tana biyan ’yan ta’adda makudan kuɗaɗe kuma tana neman gafararsu.
Ya ce lokacin da ’yan bindiga suka kai hari na farko a wata makaranta a Jihar Kaduna, sai da aka biya su naira biliyan daya kafin su sako ɗaliban da aka yi garkuwa da su.
Sannan ya yi ikirarin cewa idan gwamnan jihar ko duk wani da yake da shakku kan abin da ya fada, ya kalubalance shi, to zai fito da hujjojin da yake da su kan hakan.
El-Rufai, wanda ya mulki Jihar Kaduna tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023, ya zargi gwamnati da ƙarfafa wa ’yan bindiga gwiwa kuma ya ce babu inda aka taba yin haka kuma aka samu nasara a duniya.
Sai dai mai magana da yawun Ofishin Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro Malam Zakari Mijinyawa ya ce kalaman na tsohon gwamnan ba gaskiya ba ne.
Ya ce ba a taba samun wani lokaci da Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara, ko gwamnati a kowane mataki da ta taba biyan kudin fansa ga miyagu, masu aikata manyan laifuka ba, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.














