Gwamnatin Nijeriya ta bai wa ‘yan ƙasarta damar ƙarshe ta kwashe su daga Afirka ta Kudu

Minista Bianca Ojukuwa ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da har yanzu ba su yanke shawara game da komawa gida ba, su yi nazari a kan haɗɗuran a hankali, tana mai tuna musu cewa za a iya maye gurbin jari da aka rasa, amma ba za a iya maye gurbin rai ba.
6 Jul, 2026
‘Yansandan Nijeriya sun daƙile harin ‘yanbindiga a Sokoto, sun ƙwato AK-47

A cewar sanarwar, an gudanar da aikin ne bayan samun kiran gaggawa da ke nuna cewa ɗimbin ’yanbindiga masu ɗauke da muggan makamai sun mamaye ƙauyen Daraye.
6 Jul, 2026
Gwamnatin Nijeriya ta ƙaddamar da fara ayyukan Bama zuwa Banki da Dikwa zuwa Gamboru-Ngala

Ƙaddamar da fara aikin ya samu halartar attajirin Afirka Aliko Dangote da Mataimakin Shugaban Nijeriya Kashim Shettima da ministan ayyukan Nijeria Dave Umahi.
5 Jul, 2026
Hukumar INEC ta Nijeriya ta tsawaita aikin rajistar masu zaɓe da makwanni biyu

Hukumar INEC ta ce ta ɗauki wannan matakin ne bayan la’akari da ra’ayoyin da ta samu daga ofisoshinta na jihohi, jam’iyyun siyasa, ƙungiyoyin fararen-hula da sauran masu ruwa da tsaki.
4 Jul, 2026

Kotu ta samu mutum biyu da laifin ta’addanci a Nijeriya

Nijeriya ta ƙaddamar da masana’antar sarrafa lithium mafi girma a Yammacin Afirka a jihar Nassarawa

Amurka ta janye akasarin sojojinta da ta aika Nijeriya

Yunwa ta kai mummunan mataki da bai taɓa kai wa ba a shekaru 10 a Arewacin Nijeriya – WFP

Sojojin Nijeriya sun kashe ’yanta’adda 662, sun ceto 951 da aka sace cikin watanni uku
1 Jul, 2026
CBN ya soke lasisin ƙananan bankuna na Microfinance 46 saboda rashin cika ƙa’idoji
CBN ya ce wannan mataki zai taimaka wajen tsaftace tsarin microfinance a Nijeriya tare da ƙarfafa bankunan da ke aiki bisa ƙa’ida da ƙarfi.

1 Jul, 2026
Nijeriya ta yi alƙawarin tallafa wa ‘yan ƙasar 271 da suka dawo daga Afirka ta Kudu
Ministan Harkokin Jinƙai da Rage Talauci, Dakta Bernard Doro ya ce gwamnati na ci gaba da jajircewa wajen kare mutunci da walwalar ‘yan Nijeriya a duk inda suke.

30 Jun, 2026
Gwamnatin Nijeriya ta karɓi ‘yan ƙasar 269 da aka sake mayarwa gida daga Afirka ta Kudu
Gidan taladijin ɗin ya ambato wata sanarwar daga ma’aikatar na cewa ambassada Ali-Gombe ya miƙa saƙon gaisuwar Shugaba Tinubu yana mai tabbatar da cewa gwamnati ta duƙufa ga kare ‘yan Nijeriya a ketare.

30 Jun, 2026
Jam’iyyar adawa ta NDC a Nijeriya ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu game da rijistarta
Wannan na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan wata babbar kotun tarayya a birnin Lokoja ta jihar Kogi, ta jingine hukuncin da ta yanke daga farko da ya bai wa hukumar zaɓe (INEC) umarnin yi wa NDC rijista a matsayin jam’iyyar siyasa.

29 Jun, 2026
‘Yanta’addan Boko Haram sun kai hari makaranta sun kashe malami tare da sace dalibai a Jihar Borno
Sun yi ta buɗe wuta , inda suka kashe malami ɗaya da kuma ji wa wasu mutane ciwo kafin su yi garkuwa da wasu ɗalibai da ba a san adadinsu ba

29 Jun, 2026
Dakarun Nijeriya sun ce manyan kwamandojin DAESH sun miƙa wuya sakamakon ƙara matsin lambar soji
Rundunar ta ce ana tsare da waɗanda suka miƙa wuya a wani wuri mai tsaro, inda ake tantance su, yi musu tambayoyi da kuma gudanar da sauran matakan da suka dace bisa ƙa’idojin aikin soji.

29 Jun, 2026
An kama mutane 10 da ake zargi da kashe shugaban ƙungiyar Fulani ta MACBAN na jihar Benue a Nijeriya
An kama wadanda ake zargin ne a daren 27 ga Yuni a yayin wani aiki samame da tawagar sashen dabaru na rundunar ta gudanar a karamar hukumar Otukpo, in ji mai magana da yawun yansanda jihar Benue.

28 Jun, 2026
‘Yan bindiga sun sace ɗalibai da ma’aikata a wata makaranta a Jihar Neja
Bayanai na cewa, maharan sun afka makarantar ne da misalin karfe biyu zuwa uku na dare, inda suka tafi da dalibai da ma’aikatan, sai dai har kawo yanzu babu bayani kan adadin mutanen da harin ya shafa.

28 Jun, 2026
Sojoji sun kashe Lakurawa biyu da ƙwato makamai a Arewa Maso Yammacin Nijeriya
A cewar rundunar sojin, an ƙaddamar da aikin ne bayan samun bayanan sirri da suka nuna cewa waɗanda ake zargin na shirin kai hari kan al’ummar Sabarumawa.

28 Jun, 2026
DSS ta saki mutumin da aka tsare saboda zargin alaƙa da Boko Haram bisa kusure, ta biya shi diyya
Jaridun Nijeriya sun rawaito cewa Shugaban DSS ne ya bayar da umarnin sakin manomin, Nura Idris, wanda kuma makiyayi ne daga Karamar Hukumar Soba ta jihar Kaduna, yayin da ake ci gaba da nazari kan batutuwan waɗanda aka tsare ba bisa ƙa’ida ba.



