Nijeriya ta ce an warware ‘taƙaddamar diflomasiyyar’ da ke tsakaninta da Amurka kan rashin tsaro

Trump ya soki ƙasar yammacin Afirkan a watan Oktoba da Nuwamba, yana cewa Kiristoci a can suna fuskantar ‘kisan ƙare dangi’ a cikin mawuyacin halin rashin tsaron Nijeriya.

Newstimehub

Newstimehub

22 Dec, 2025

683a82403c464959c6b252987212fe83cfee1480fb5355d3eccde9858e8d43a1 main

Gwamnatin Nijeriya ta ce ‘an warware taƙddamar diflomasiyyar’ da ta faru kwanan nan tsakaninta da Amurka, inda Shugaba Donald Trump ya yi barazanar shigar da sojoji kan zargin azabtar da Kiristoci,

Trump ya soki ƙasar yammacin Afirkan a watan Oktoba da Nuwamba, yana cewa Kiristoci a can suna fuskantar ‘kisan ƙare dangi’ a cikin mawuyacin halin rashin tsaron Nijeriya.

‘Rikicin diflomasiyya da ya faru kwanan nan da Amurka an warware shi kusan gaba ɗaya ta hanyar mu’amala mai ƙarfi da girmamawa, wanda ya haifar da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Amurka da Nijeriya,’ in ji Ministan Yaɗa Labaran Nijeriya Mohammed Idris a taron manema labarai na ƙarshen shekara a babban birnin tarayya, Abuja.

Gwamnatin Nijeriya da masana masu zaman kansu sun ƙi goyon bayan fassara matsalar rashin tsaron ƙasar a matsayin azabtarwa ta addini.

Yarjejeniyar agaji

Maganganun Idris sun biyo bayan karɓar tawagar wakilan majalisar dokoki ta Amurka da Nijeriya ta yi a farkon wannan wata.

A makon da ya gabata, Nijeriya ta kasance cikin kasashen da gwamnatin Trump ta sanya musu takunkumin biza da na shige-da-fice.

Nijeriya na fuskantar barazanar ‘yanta’adda a arewa maso gabas, da kuma ƙungiyoyin ‘yan fashi da makami waɗanda ke sata a ƙauyuka da sace mutane domin neman fansa a arewa maso yamma.

A lokacin da yake magana da ‘yanjarida, Idris ya kare wata sabuwar yarjejeniyar agaji wadda za ta sa Washington ta bayar da dala biliyan 2.1, abin da Ma’aikatar Harkokin Waje ta Amurka ta bayyana a matsayin ‘wanda zai fi mayar da hankali wajen inganta kiwaon lafiyar mabiya addinin Kiristanci.’

‘Kowane ɗan Nijeriya zai kasance mai cin gajiyar wannan tsari,’ in ji Idris.