Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar, ya bukaci ƙasashen yankin Gulf masu samar da mai da iskar gas da su dauki Nijeriya a matsayin abokiyar hulɗa maimakon abokiyar hamayya. Ya ce haɗin kai tsakanin ɓangarorin zai iya taimakawa wajen samar da wata hanya ta samar da mai musamman a lokacin rikice-rikicen duniya.
Jawabin nasa ya zo ne yayin da rikicin da ke gudana a Gabas ta Tsakiya ya kawo cikas ga jigilar man fetur ta mashigin Hormuz, wata muhimmiyar hanya da kusan kashi biyar na man da duniya ke amfani da shi ke wucewa. Wannan matsala ta sa wasu kamfanoni dakatar da jigilar kayayyaki, lamarin da ya haifar da tashin farashin mai a kasuwannin duniya.
Tuggar ya ce Nijeriya na da manyan rumbunan mai da ba a yi amfani da su ba, wanda zai iya ba ƙasashen Gulf damar samun danyen mai da iskar gas a lokacin da hanyoyin samar da kayayyaki ke fuskantar barazana. Ya jaddada cewa zuba jari da haɗin kai da Nijeriya zai taimaka wajen faɗaɗa kasuwanci da kuma tabbatar da wadatar makamashi a duniya.
A cewarsa, samar da man fetur a Nijeriya ya ƙaru zuwa kusan ganga miliyan 1.7 a rana daga miliyan 1.4 lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki a 2023, duk da ƙalubalen sata da lalata bututun mai da ƙasar ta dade tana fuskanta.














