An shiga cikin yanayi na makoki a birnin Zinder bayan ruwan sama mai ƙarfi ya haddasa ambaliyar ruwa wadda ta yi sanadin mutuwar yara huɗu tare da lalata gidaje da dama.
Ruwan ya fara sauka da misalin ƙarfe 4:45 na asuba, inda aka aka tafka ruwan da ba a taɓa ganin irinsa ba a yankin. A Tabkin Kalgo an samu milimita 170 na ruwan sama, yayin da a Angoual Makko aka samu 162.2 mm, sai kuma a Zinder Ville aka samu 143 mm — waɗannan duk sun ninka matsakaicin ruwan damina na shekara.
Kafin a farga, tituna sun zama kamar koguna, gidaje kuma sun zama tarko ga mazauna cikinsu. A wani mummunan lamari, wani uba ya samu nasarar ceto yaransa biyu daga cikin huɗu kafin bangon gidansa da aka gina da laka ya ruguje, inda ginin ya hallaka sauran yaran biyun. An kai gawawwakin yaran duka zuwa ɗakin ajiye gawa na asibiti.
Asarar rayuka da dukiya
Kididdigar wucin gadi ta nuna cewa yara huɗu, masu shekaru tsakanin uku da takwas, ne suka rasu. Bayan rasa rayuka, ruwan saman ya rushe gidaje da dama tare da nutsar da unguwanni gaba ɗaya. Masana sun tabbatar da cewa adadin ruwan da aka samu a ranar Asabar ya yi matuƙar yawa fiye da kowane lokaci.
Lamarin ya sake nuna irin raunin gidajen laka da ake ginawa a yankunan talakawa wajen jure irin wannan ruwan sama.
Hukumomi sun shiga don agaji
Sakamakon wannan lamarin da ya faru, Daraktan Birnin Zinder tare da manyan jami’an gari sun ziyarci unguwannin da abin ya fi shafa tun da safe domin tantance asara da ganawa da iyalan da abin ya rutsa da su da kuma tsara matakan agaji.
“Muna bin diddigin halin da ake ciki tare da bayar da cikakken tallafi ga waɗanda abin ya shafa,” in ji jami’an birnin, suna mai kira ga ƙarin haɗin kai domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa.