Ministan Tsaron Isra’ila ya ce zai jefa wa ‘yan Houthi annoba 10 da aka jarrabi Misirawa a Injila

Katz na Isra’ila ya ba da misali da wani bayanin baibul kuma ya yi gargadi game da azabtarwa da mayar da kakkausan martanin ga ‘yan Houthi na Yemen.

Newstimehub

Newstimehub

4 Sep, 2025

3c141a1af3a467f9771356cece31c2df209ea2d9f602453cf58819629e80e06a

Ministan Tsaron Isra’ila ya sha alwashin azabtar da ‘yan Houthi na Yemen da irin “annoba 10 da aka jarabci Misirawa da su” wanda baibul ya ba da labarinsu, bayan da ‘yan Houthin suka zafafa kai hare-haren makamai masu linzami a kan Isra’ila.

A ranar Alhamis, Israel Katz ya wallafa a shafin X cewa, “‘Yan Houthi suna sake harba makamai masu linzami a kan Isra’ila. “Annobar duhu da annobar ‘ya’yan fari – za mu azabtar da su da duka na’u’kan annoba goma,” kamar yadda Katz ya wallafa a shafin X a ranar Alhamis.

Ya ambaci bala’o’i 10 da baibul ya lissafa – kama daga mayar da ruwa ya zaman jini zuwa mace-macen ‘ya’yan fari – waɗanda Surar Exodus ta baibul ta yi bayanin cewa Allah ne Ya saukar wa Masar don tilasta Fir’auna ya ‘yanta Isra’ilawa bayi.

To amma me Katz ke nufi da ba da misali da waɗannan misalan na Baibul?

Ya ambato azabobin da Allah Ya aike wa Misirawa da suka haɗa da: duhu, ƙanƙara, tsutsotsi, mutuwar ‘ya’yan fari – wasu jerin bala’o’i masu tsanani a matsayin wani gargadi da aka bayyana cikin Baibul. Ya yi bayanin halaka gaba ɗaya ba tare da sassauci ba.

Wannan yana da muhimmanci saboda Isra’ila tuni tana fuskantar zarge-zarge masu tsanani na kashe dubban fararen hula da kuma watsi da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa a kan yaƙin.

Masana da ƙwararru sun ce yaƙin sojan da Isra’ila ke yi a Gaza ya cika ma’anar shari’ar kisan ƙare dangi.

Majalisar Dinkin Duniya ta riga ta tabbatar cewa takunkumin hana shigar da abinci da Isra’ila ta sanya ya haifar da matsalar yunwa a Gaza, inda ɗaruruwan mutane suka mutu saboda yunwar da aka ƙaƙaba musu.

Ƙungiyar Ƙwararru kan Kisan Ƙare Dangi ta Duniya, wacce ita ce babbar kungiyar masana a kan kisan ƙare dangi, ta zartar da ƙuduri a wannan makon tana bayyana cewa manufofi da ayyukan Isra’ila a Gaza sun cika ƙa’idojin da aka shimfida a Mataki na II na Yarjejeniyar Kisan Kare Dangi ta Majalisar Dinkin Duniya ta 1948.

Kashi 86 cikin 100 na mambobin da suka kaɗa ƙuri’a sun goyi bayan wannan ƙudurin.