An tilasta wa Jakadan Isra’ila a Senegal, Yuval Waks, barin harabar harabar wata jami’a a Dakar a ranar Talata bayan ɗalibai sun yi zanga-zanga kan zuwansa tare da rera taken goyon bayan Falasɗinu, kamar yadda wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna.
An gayyaci Waks don yin jawabi a wani taro kan dabarun hulɗar ƙasa da ƙasa a Jami’ar Cheikh Anta Diop (UCAD), wacce ita ce mafi girma kuma mafi shahara a fannin ilimi a ƙasar.
Amma da ya iso, ɗaruruwan dalibai sun taru a wajen dakin taron, suna rera taken kalmar “’Yantar da Falasɗinu”, “’Yantar da Gaza” da kuma “Isra’ila mai aikata laifukan yaƙi”.
Bidiyoyin da aka wallafa a intanet sun nuna dalibai suna ɗaga tutocin Falasɗinu tare da yin ihu ga jakadan da aka naɗa kwanan nan, suna hana shi yin jawabin da aka shirya.
Jami’an tsaro sun raka Waks yayin da yake fita daga jami’ar, inda ya bar harabar ba tare da ya yi jawabin ga mahalarta ba. Masu zanga-zangar sun ci gaba da binsa, suna rera taken da ɗaga tutoci har ya bar wajen.
Waks, wanda kuma yake matsayin jakadan Isra’ila da ke kula da ƙasashen Gambiya, da Guinea, da Guinea-Bissau, da Cape Verde da Chadi, ya gabatar da takardun aikinsa ga Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye a ranar 8 ga Mayu.









