Ma’aikatar Shari’ar Jamhuriyar Nijar ta yi bayani game da matakin da gwamnatin ƙasar ta ɗauka na rusa ƙungiyoyin ƙwadago huɗu da ke fannin shari’a.
Kamfanin dillancin labaran ƙasar, (ANP) ya ambato wata sanarwar da Ministan Shari’ar ƙasar, Alio Daouda ya fitar tana cewa an yi amannar cewa ƙungiyoyin ƙwadagon huɗu ba sa aiki domin inganta aikin ɓangaren shari’a domin kare muradun al’umma.
Ƙungiyoyin ƙwadagon sun haɗa da ƙungiyoyin SAMAN da SNAJ da SYNCAT da kuma UMAN.
Sanarwar ta ƙara da cewa maimakon ƙoƙarin kare muradun al’umma, ƙungiyoyin na aikin kare muradun kansu ne, lamarin ke ƙasa-ƙasa da harkar yi wa ƙasa hidima.