Rahotanni daga jihar Kebbi sun ce aƙalla sojoji 11 da ɗansanda ɗaya sun rasa rayukansu bayan da ‘yanbindiga suka yi musu kwanton-ɓauna a garin Giro Masa da ke ƙaramar hukumar Shanga. Lamarin ya faru ne a daren Talata lokacin da jami’an tsaro suka nufi wani wuri bayan samun bayanan sirri cewa maharan na taruwa a can domin kai hari, sai dai daga bisani aka gano bayanan ba gaskiya ba ne.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa jami’an tsaron sun tafi ne da niyyar kare al’umma bayan rahoton da suka samu, amma a hanyarsu ne suka faɗa tarkon ‘yanbindiga. Rahotanni sun kuma ce maharan sun ƙona motocin soji guda biyu. Gwamnan ya kai ziyara asibitin koyarwa da ke Birnin Kebbi inda aka kai waɗanda suka jikkata, sannan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta biya kuɗin jinyarsu tare da tallafa wa iyalan jami’an da suka mutu.
Idris ya bayyana harin a matsayin dabbanci da babban rashi ga jihar, yana mai cewa gwamnati ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen tallafa wa jami’an tsaro da ƙarfafa matakan tsaro. Ya kuma yi alkawarin ganawa da babban hafsan tsaron Nijeriya a Abuja, tare da cewa gwamnati za ta maye gurbin motocin aikin da aka ƙona. Har ila yau, ya yabawa sojojin da ke bakin aiki tare da ƙarfafa musu gwiwa kada su ja da baya.
Wannan hari na daga cikin jerin hare-hare masu muni da ‘yanbindiga da ‘yan ta’adda ke kaiwa a arewacin Nijeriya, inda sau da dama jami’an tsaro ke rasa rayukansu. An tuna cewa a watan Yuni 2025 ma sojoji 17 sun mutu a wani artabu da ‘yanfashin daji a jihar Neja, yayin da a arewa maso gabashin ƙasar hare-haren Boko Haram da ISWAP ke ci gaba da jawo asarar rayuka a sansanonin soji.














