Hukumomi a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo sun fara bincike bayan kama makudan kudade a filin jirgin sama na N’djili, a wani mataki na yaki da laifukan kudi. Ministan shari’a, Guillaume Ngefa, ya tabbatar da cewa an kama kusan dala miliyan 1.9, yayin da wasu rahotanni ke cewa kudin na iya kaiwa sama da dala miliyan 3.5.
Ministan ya ba da umarnin a rufe kudaden tare da kula da su bisa doka, sannan a tattara cikakken rahoto kan yadda aka kama su, ciki har da gano wanda abin ya shafa da jami’an da suka halarta. Ya jaddada cewa dole ne a bi dukkan matakan shari’a domin tabbatar da gaskiya.
Bisa dokar yaki da safarar kudade ta haramtacciya, za a mikawa Babban Bankin Kongo wadannan kudade, sannan a tura bayanan shari’ar ga hukumar binciken harkokin kudi (CENAREF). Haka kuma, an umarci a fara shari’a domin binciken asalin kudaden da kuma ko akwai laifi a ciki.
Wannan na zuwa ne bayan shugaban kasa Félix Tshisekedi ya kafa wata kotu ta musamman domin yaki da laifukan tattalin arziki da suka hada da rashawa, zamba da safarar kudade, a kokarin kara tsaftace tsarin kudi na kasar.














