Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja na Nijeriya ya yi hatsari bayan sauka daga layinsa

Zuwa lokacin wallafa wannan labari dai hukumar kula da layukan dogo ta Nijeriya ba ta ce komai a kan lamarin ba, sannan ba a san musabbabin faruwar hatsarin ba.

Newstimehub

Newstimehub

26 Aug, 2025

beaadb6d5269fbb7bf027de4a0ca17f4e2d6082f38e2e6557de020fd50fe6d7d main

Jirgin ƙasan da ke zirga-zriga tsakanin Abuja zuwa Kaduna a Nijeriya ya yi hatsari bayan da ya sauka daga layinsa a ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a garin Asham, kamar yadda wani mai amfani da shafin Facebook, Imo Onyekwereya wallafa faruwar lamarin kai-tsaye ta bidiyo a shafinsa.

Hatsarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safe, jim kaɗan bayan tashin jirgin daga Abuja zuwa Kaduna.

A cikin bidiyon, ana iya ganin yadda taragun jirgin suka tuntsura, kuma mutane sun taru a wajen suna kallon abin da ya faru da ƙoƙarin aikin ceto, yayin da wasu da suka fi kama da fasinjoji na tsaye cirko-cirko.