Jami’an tsaron Nijeriya sun kama shugabannin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru, Abu Barra da Mamuda

“Nijeriya ta daɗe tana neman waɗannan mutanen biyu ruwa-a-jallo, haka kuma ‘yan ta’adda ne da ƙasashen duniya ke nemansu,” a cewar Malam Nuhu Ribadu.

Newstimehub

Newstimehub

16 Aug, 2025

65e125511207be0a141ee4c0475f99195cc0ed0a3810bb8037de9220cf3dd5e5

Hukumomin tsaro a Nijeriya sun kama manyan shugabannin ƙungiyar ‘yan ta’adda ta Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda, a cewar mai bai shugaban ƙasar shawara kan harkokin tsaro.

Malam Nuhu Ribadu , wanda ya jagoranci shugabannin tsaro na ƙasar wajen gudanar da taron manema labarai a ranar Asabar a Abuja, ya ce an kama Mahmud Muhammad Usman (Abu Barra) da Abubakar Abba (Mahmud Al-Nigeri/Malam Mamuda).

“Ina mai farin cikin shaida muku cewa mun yi nasarar kammala aikin yaƙi da ta’addanci mai cike da hatsari da tattara bayanan sirri, wanda ya kai mu ga kama manyan shugabannin ƙungiyar da aka fi sani da Ansaru, wato reshen Al-Qaeda da ke Nijeriya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa an kama mutanen biyu ne tsakanin watan Mayu zuwa watan Yulin 2025, yana mai cewa kamun nasu ya zama sanadiyar wargajewar cibiyar bayar da umarni ta ƙungiyar Ansaru.