Ƙasar Iran ta yi kira ga ƙasashen Gabas ta Tsakiya su kafa sabon ƙawancen tsaro da na soji wanda ba zai haɗa da Amurka da Isra’ila ba, a wani yunƙuri na sauya tsarin tsaron yankin. Kakakin hedkwatar Khatam al-Anbiya, Ebrahim Zolfaghari, ya ce lokaci ya yi da ƙasashen yankin za su riƙa kare kansu tare ba tare da dogaro da ƙasashen waje ba.
Ya bayyana hare-haren da Amurka da Isra’ila ke kai wa Iran a matsayin wani sabon yanayi da ke buƙatar haɗin kai tsakanin ƙasashen Musulmai. A cewarsa, dole ne a gina sabon tsarin tsaro bisa haɗin kai na addini da yankin, domin cimma dawwamammen zaman lafiya da tsaro.
Zolfaghari ya jaddada cewa dogaro da ƙasashen waje bai kawo cikakken tsaro ba, yana mai kira ga ƙasashen Larabawa da na Musulmai su kafa yarjejeniya ta bai-ɗaya. Wannan kira na zuwa ne yayin da Iran ke fuskantar matsin lamba na soja a sakamakon rikicin da ke gudana.
A halin yanzu dai, rikicin ya ƙara tsananta bayan hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai, inda Iran ke mayar da martani da makamai masu linzami da jiragen drone. Duk da haka, har yanzu ba a san ko ƙasashen yankin za su amince da wannan sabon ƙawance ba, musamman ganin alaƙar tsaro da suke da ita da Amurka.














