Hotunan yadda dubban Musulmai a ƙasashen duniya suka yi murnar Maulidin Annabi

Musulmai a ƙasashe irin su Turkiyya, Falasɗinu, Masar, Somaliya, Iraƙi da wasu wurare sun yi tarukan murna zagayowar Maulidin Annabi Muhammad a salo daban-daban.

Newstimehub

Newstimehub

5 Sep, 2025

221a3039ae5392db07c220f576b596f28dbf35a67aca08ef5cb0a882d4b94a1e

Mutane a ƙasashen Musulmai sun yi bikin Maulidin Annabi, wato murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW), ta hanyoyi daban-daban bisa aƙidunsu.

A ƙasashe kamar Turkiyya, Falasɗinu, Masar, Somaliya, Iraƙi da sauran wurare, an yi tarukan Mauludi ta hanyoyi da dama, inda wasu suka gabatar da addu’o’i da lakcoci ko tattaki don murnar wannan rana mai muhimmanci.

Ga wasu daga cikin hotunan yadda bikin Maulidin ya kasance:

Turkiyya

A biranen Ankara, Istanbul da sauran wurare, Musulmai sun taru don yin addu’o’i duk don murnar zagayowar ranar haihuwar Annabi Muhammad (SAW).

93c3347dceafebdde65f4818fd605a1f891e62bf8b41b228a486be800653a923
d60b0a2c3b9410f69da990fd9aa5f0fe8948b9927e44dd3db592c4a4ad16eba5

Falasɗinu

Duk da tsananin mamayar Isra’ila, Falasdinawa ba su yi ƙasa a gwiwa ba wajen murnar wannan rana, inda suka tafi Tsohon Birnin Ƙudus a yankin Gaɓar Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, don yin biki a Masallacin Ƙudus.

fcd28a755f3ef4c6c81670c9f81d3737e86387033d8f75dcdf69eb1a7abae55f
2025 09 04T135616Z 1758704288 RC2ZKGAB7WLO RTRMADP 3 RELIGION PROPHET JERUSALEM

Masar

Musulmai Sufaye a Masar sun cika titunan birnin Alkahira da sauran manyan yankuna don murnar wannan rana ta hanyar al’adunsu na Sufanci, wanda ya haɗa da rera waƙoƙin addini.

2e509b4421e567b584cd5155ba40b1cb1cd0bf4b480816dde3173b191bf4dde0
ab962282e4d57413d30ca95a200ecc0cef10c7e2f1f9a1914e11c21a95bb0f81