Hukumar layin dogo ta Nigeria (NRC) ta tabbatar da cewa wasu fasinjoji sun ji rauni bayan wani hatsari da ya faru kusa da tashar Asham a layin Abuja zuwa Kaduna da safiyar Litinin. Lamarin ya faru ne lokacin da wani ɓangaren jirgin ya bugi wani sashen da ke gabansa yayin tafiya.
Babban daraktan hukumar, Kayode Opeifa, ya ce hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe. Ya ƙara da cewa an garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin samun kulawa, inda ya jaddada cewa ba a samu asarar rai ba a wannan lamari.
Hukumar ta ce an ɗauki matakan gaggawa nan take, inda aka tura ma’aikata da masu ruwa da tsaki zuwa wurin domin shawo kan lamarin. Haka kuma, cibiyar bincike kan kariya ta isa wurin domin fara bincike kan musabbabin hatsarin kamar yadda dokoki suka tanada.
Daga baya jirgin ya ci gaba da tafiya zuwa tashar Idu da jinkirin minti 38 bayan cire ɓangaren da ya lalace. NRC ta tabbatar wa jama’a cewa tsaron fasinjoji ne ke kan gaba a aikinta, kuma za ta ci gaba da ɗaukar matakan da suka dace domin kauce wa irin wannan lamari a gaba.














